Isa ga babban shafi
Ebola

Ana gab da samar da maganin warkar da Ebola

Masana ilimin kimiya na gab da samar da maganin warkar da cutar Ebola bayan gwajin wasu kyayoyin magunguna da suka yi kan wani adadi na jama’ar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo mai fama da cutar.

Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a Congo
Wasu daga cikin jami'an kiwon lafiya da ke yaki da Ebola a Congo (WHO)
Talla

Cibiyar Kula da Lafiya ta Amurka ta bayyana cewa, tun a cikin watan Nuwamban da ya gabata ne, aka fara bincike game da magungunan warkar da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, kodayake an samu tsaiko wajen ci gaba da binciken, amma a yanzu, magungunan sun yi tasiri kan jama’ar da ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Magungunan samfurin REGN-EB3 da kuma mAb114, su ne na farko da aka tabbatar da sahihancinsu a kimiyance don yaki da Ebola, yayinda suka taka rawa wajen rage mace-macen mutanen da ke dauke da kwayoyin cutar Eobala kamar yadda Darektan cibiyar Lafiyar ta Amurka, Anthony Fauci ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.

Darektan ya ce, da fari sun kudiri aniyar gwajin magungunan kan mutane a 725, amma aka takaita adadinsu zuwa 681, yayinda kawo yanzu aka tantance sakamakon gwajin kan mutane 499.

Bayan tantance magungunan na REGN-EB3 da mA114 kan mutanen 499, an gano cewa, an samu raguwar mace-mace da kashi 34 tsakanin wannnan adadi kadai.

Yanzu haka, nan da watan Satumba zuwa Oktoba ne ake sa ran kammala tantance sauran mutanen kafin daga bisani a wallafa sakamakon binciken.

Akalla cutar Ebola ta kashe mutane dubu 1 da 800 tun bayan sake barkewarta a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Congo a cikin watan Agustan bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.