Yayin gabatar da binciken da suka yi a Mexico, wajen taron masana cutar na 10 a Mexico, masanan sun bayayna ceawar maganin da aka samar mai kamar tsinke ashana, na iya zama wani gagarumin cigaba wajen rage kamuwa da cutar.
Darakta Janar na Cibiyar gudanar da binciken, Mike Robertson yace amfani da maganin zai taimaka wajen sanya wasu sinadaren da za su iya kare jama’a daga kamuwa da cutar.
Majalisar Dinkin Duniya tace an samu raguwar masu kamuwa da cutar zuwa kashi daya bisa uku daga shekarar 2017 zuwa 2018, adadin da ya kai 770,000 a fadin duniya.