Isa ga babban shafi
Lafiya

Rotary ta ware Dala miliyan 100 domin yaki da Polio

Kungiyar Agaji ta Rotary ta sanar da bada agajin Dala miliyan 100 a matsayin gudumawa domin kawar da cutar polio daga kasashen duniya.

Najeriya da Afghanistan za su karbi kaso mai yawa wajen ci gaba da yaki da cutar Polio
Najeriya da Afghanistan za su karbi kaso mai yawa wajen ci gaba da yaki da cutar Polio Getty Images/Ranplett
Talla

Bada wannan gudumawa na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar agajin tare da kawarta, GPEI da ke yaki da cutar polio suka gabatar da wani mataki na karshe wanda zai kawo karshen cutar, ganin yadda Najeriya ta kama hanyar cika shekaru 3 ba tare da samun wani wanda ya kamu da ita ba, matakin da ake ganin zai kawo karshen cutar a nahiyar Afrika baki daya.

Shugaban Kwamitin yaki da cutar Polio a Najeriya, Dr. Tunji Funsho ya ce, ci gaba da bada rigakafin cutar a jihohin da ke fuskantar barazana na da matukar tasiri.

Kungiyar ta bayyana cewar daga cikin Dala miliyan 100 da za ta bayar, Afghansitan za ta karbi sama da Dala miliyan 16, yayinda Najeriya za ta karbi sama da Dala miliyan 10, sai kuma Pakistan mai sama da Dala miliyan 25.

Sauran kasashen da za su amfana da kudaden sun hada da Chadi da Mali da Kenya da Iraqi da Somalia da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Sudan ta Kudu da Syria da kuma Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.