Isa ga babban shafi
Lafiya

Shin kun san abincin da ya dace da jikinku?

Masana kimiya sun bayyana irin abincin da ya dace mutane su rika ci domin samun koshin lafiya wadanda suka hada da nau'ukan gyada da wake da kayan marmari da kuma rage yawan cin nama da shan suga.

Masana sun bukaci jama'a da su rika cin abinci mai gina jiki domin samun koshin lafiya
Masana sun bukaci jama'a da su rika cin abinci mai gina jiki domin samun koshin lafiya DR
Talla

Masanan sun ce, muddin jama’a suka bi wannan hanyar, za a magance matsalar yadda mutane miliyan 11 ke mutuwa kowacce shekara, sakamakon cutar da ke da nasaba da abincin da suke ci, yayin da kuma za a rage yawan fitar da sinadarin da ke gurbata muhalli.

Jagoran masu binciken, Farfesa Tim Lang na Jami’ar London, ya ce abincin da jama’a ke ci da kuma yadda ake sarrafa su, ke nuna halin lafiyar jama’a da kuma muhalli.

Masanan sun ce, akasarin cututtukan da ake fama da su na da nasaba da abincin da jama’a ke ciki, cikinsu har da kibar da ta wuce kima da cutar hawan jini da kuma nau’oin cutar kansa.

Walter Willet na Jami’ar Amurka ya ce, yayin da wasu mutane ke kamuwa da cututtukan da ke da nasaba da abincin da suke ci, yanzu haka akalla mutane miliyan 800 a fadin duniya ke fama da karancin abincin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.