Isa ga babban shafi
Lafiya

WHO ta ce rabin al’ummar duniya ba sa samun kulawar lafiya

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, WHO, ta ce rabin al’ummar duniya ba sa samun cikakken kulawar lafiya na yau da kullum, wanda ke tursasawa da dama daga cikinsu shiga talauci saboda biyan kudadden asibiti da magunguna da ba su da hali.

Rabin al’ummar duniya ba sa samun kulawar lafiya na yau da kullum
Rabin al’ummar duniya ba sa samun kulawar lafiya na yau da kullum REUTERS/Pilar Olivares
Talla

WHO ta ce mutum miliyan 800 na kashe akalla kashi 10 cikin 100 na kudadden da ke shigo musu a rana wajen nemawa kansu da yaransu lafiyar, wanda ke nakasa rayuwar mutum miliyan 100 da a ranar ke samun kasa da dala 2.

Rahotan hadin-guiwa na WHO da Bankin duniya ya ce abu ne da ba za a zura ido ba, ganin sama da rabin al’ummar duniya har yanzu basa samun kyakyawan kulawar lafiya na yau da kullum.

Shugaban Bankin Jim Yong Kim a cikin Rahotan ya ce idan ba a mayar da hankali ba, wannan lamari ba fannin kiwon lafiya kawai zai ci gaba da nakasawa ba, zai hana kokarin da ake na kawo karshan talauci a duniya.

Kim ya ce wajibi ne kasashe su tashi tsaye domin inganta matsalolin kiwon lafiya.

Rahotan na wannan karon ya ce an samu ci gaba a wannan karni a fanonnin karban allurar Rigakafi da magani SIDA da tsarin amfani da gidan sauro da magunguna hana daukan juna biyu.

Sai dai akwai wagegen gibi na samun wadatattun kiwon lafiya a yankin kudu da sahara da kudancin Asia a cewar Rahoton.

A wasu yankunan tsarin kiwon lafiya na yau da kullum da ya danganci kayyade iyali da rigakafi ga kananan yara akwai su, sai dai iyalai na shan wahala wajen samun kudadden karbansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.