Isa ga babban shafi
MDD

''Mutane Miliyan 7 taba sigari ke hallakawa a shekara''

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da miliyan 7 taba sigari ke hallakawa a kowacce shekara, bayan asarar kudin da ya kai kusan Triliyon 1.5.

Taba sigari na hallaka miliyoyin mutane a duniya
Taba sigari na hallaka miliyoyin mutane a duniya REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Shugabar hukumar mai barin gado, Margareth Chan ta bayyana haka, yayin da yau ake bikin ranar yaki da busa tabar wadda ta zama annoba ga duniya.

Majalisar ta ce bayan illar da tabar ke yiwa masu zukar ta, har ila yau tana yiwa muhalli illa sosai ta hanyar gubar da ke fita daga cikin ta.

Jami’ar ta ce taba sigari na haifar da talauci da kuma jefa jama’a cikin halin kunci.

WHO dai ta jimma tana fafutakar gani alkalluman masu shan sigari ya ragu a duniya saboda barazanar da ya ke yi ga rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.