Isa ga babban shafi
lafiya

Taron yaki da cutar kanjamau a Durban

Masana kimiya da kungiyoyin agaji sama da 18,000 suka soma taron yaki da cutar Sida a birnin Durban na kasar Afrika ta kudu inda za su tattauna kalubalen da yaki da cutar ke fuskanta da kuma binciken samo maganin cutar.

Cutar HIV na ci gaba da yaduwa tsakanin manyan mutane musamman matasa
Cutar HIV na ci gaba da yaduwa tsakanin manyan mutane musamman matasa MATHEW KAY / AFP
Talla

A karon farko kenan tun lokacin da marigayi Nelson Mandela ya kaddamar da yaki da cutar shekaru 16 da suka gabata, ake gudanar da taron a Afrika ta Kudu .

Taron dai ya kunshi masana daga sassan duniya kan yadda za a magance cutar da ta lakume rayukan mutane sama da miliyan 30 a shekaru 35.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon na cikin mahalarta taron .

A kwanan baya ne dai masana kimiya suka kaddamar da aikin binciken gano maganin da zai warkar da cutar Sida da wasu ke wa kirari da kabari salamu alaikum.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta kayyade hasashen fatar kawo karshen cutar a 2030. Sai dai kuma maharta taron na Durban na bayyana fargaba akan kalubalen da suke fuskanta wajen yakar cutar.

Kusan mutane miliyan 37 ne dai ke dauke da cutar HIV a duniya kuma yawancinsu na kasashen Afrika dake yankin kudu da sahara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.