Matashin da ke amfani da hannun batir a Gombe (2)
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora ne kan na makon jiya, inda ya tattauna da matashin nan da aka yanke masa hannaye a India bayan malaminsa na makarantar allo ya daure hannayen har sai da suka rube.
Yanzu haka mashin mai suna Zubairu Yusha'u na amfani da hannun batir.