Ilimi Hasken Rayuwa
Takaddama kan abincin da aka sauya wa kwayar halitta
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:34
Shirin ilimi hasken rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris na wannan mako ya tattauna ne kan takaddamar da kasashen duniya ke yi game da abincin da aka sauya wa kwayar halitta, in da kasashen Turai suka ki amincewa a shigo musu da nau'insa saboda matsalar da ke tattare da shi. Sai dai a yayin da ake wannan takardar, an shigo da irin wannan abinci a Najeriya, in da hukumomi ke gudanar da bincike. Masana sun gargadi cewa amfani da irin wannan abinci na haifar da illa ga lafiyar dan Adam kamar cutar sankara ko Kansa.