Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya yi nazari ne akan rikicin da ke tsakanin Apple da Samsung, manyan Kamfanonin samar da Wayoyin Salula a Duniya. Apple da Samsung sun dade suna hammaya da juna tsawon shekaru uku, inda Apple ke neman kotu ta haramta sayar da wayoyin salula mallakar Samsung a Amurka saboda zargin kamfanin na Samsung da satar fasaharsa.
Yanzu haka kuma akwai masu taimakawa Alkali yanke hukunci da suka bukaci kamfanin Samsung ya ba Apple kudin diyya dala sama da 119, kasa da kudi Dala Biliyan biyu da Kamfanin na Apple ya nema saboda zargin Samsung da satar fasaharsa. Shirin ya tattauna da masana Fasaha akan wannan batu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu