Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Facebook ya yi Bikin cika shekaru 10

Wallafawa ranar:

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya yi bayani ne akan dandalin sada zumunta na Facebook a Intanet wanda ya yi bikin cika shekaru 10. A ranar Talata ne 4 ga watan Fabrairu a shekarar 2004 wasu daliban makarantar Jami’ar Harvard guda biyar suka kaddamar da shafin Facebook domin yin mu’amula da sada zumunci tsakaninsu.

Dandalin sada zumunta na Facebook
Dandalin sada zumunta na Facebook REUTERS/Dado Ruvic/Files
Talla

Da farko an takaita shafin ne ga daliban Harvard a Amurka daga baya kuma aka fadada dandalin a yankin Boston har zuwa ga Jami’o’i a Amurka daga nan Facebook ya koma na kowa da kowa a fadin duniya.

Yanzu haka a cikin lokaci kalilan Facebook ya samu mutane sama da Biliyan da ke mu’amula da shafin, yanzu ma kamar hanya ce wasu suka dauka ta tafiyar da rayuwarsu.

Wasu alkalumma da aka fitar game da aiki a Intanet an bayyana cewa sama da kashi 20 na masu amfani da Intanet a lokaci guda za’a isko suna mu’amula ne da shafin Facebook.

Facebook ya ba mutane a sassa daban daban na duniyar damar haduwa su yi mu’mula ko ta abokantaka ko soyayya ko huldar kasuwanci.

Shafin Facebook yace mutanen da ke mu’amula da dandalin sun kai mutane Biliyan 1 da Miliyan 23 hadi da mutane Miliyan 945 da suke amfani da shafin na Facebook a wayoyinsu na Salula.

Sai dai wani bincike da Kamfanin Facebook ya sa aka gudanar masa an gano kusan kashi 25 na masu mu’amula da shufin da suka kaurace ‘yan shekaru 13 zuwa 17 yayin da kuma shafin ya samu karuwar mutane ‘yan sama da shekaru 55.

A shekarar 2013 kamfanin Facebook ya ruwaito cewa ya samu ribar kudi dala Miliyan 523 fiye da ribar da kamfanin ya samu a shekara ta 2013.

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya tattauna da wasu da ke amfani da Facebook akan yadda dandalin ya shafi rayuwarsu sannan kuma Shirin ya zanta da masana dangane da hamayya da Facebook ke yi da sauran dandalaye irinsu Twitter da Google +.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.