Pakistan-Amurka
Harin Amurka ya hallaka mutane hudu a Pakistan
Wasu hare haren Amurka sun kashe mutane hudu a kasar Pakistan da safiyar yau Laraba, inda kuma wasu mutane hudu suka mutu a wani hari da kuramen jiragen Amurka suka kai a Chashma da ke Arewacin Waziristan na yankin da mayakan Taliban ke buya.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni na nuna cewa daya daga cikin manyan mayakan kungiyar ya mutu a harin, ko da yake ba a ga wata alama da ta tabbatar da hakan ba.
“Akalla mutane shida ‘yan kungiyar a ka kashe aka kuma raunata wasu biyu.” Inji wani jami’in tsaron a yankin Miranshah.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu