Isa ga babban shafi

Chelsea ta karkata akalarta wajen sayen Martinez bayan rasa Osimhen

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shiga sahun masu zawarcin Lautaro Martinez na Inter Milan a wani yunkuri na maye gurbinsa da Victor Osimhen na Najeriya da ta shafe tsawon lokaci ta na neman sayenshi ba tare da ta yi nasara ba.

Dan wasan gaba na Inter Milan Lautaro Martinez.
Dan wasan gaba na Inter Milan Lautaro Martinez. © Luca Bruno/AP
Talla

Ko a kakar wasan da ta gabata, anga yadda Chelsea ta dauki lokaci mai tsawo ta na fatan sayen Osimhen daga Napoli amma aka gaza nasarar tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

Ana dai ganin Chelsea ta karkata akalarta zuwa yunkurin sayen Martinez ne don gujewa sake fuskantar biyu babu a cinikin na Osimhen bayan bude kasuwar musayar ‘yan wasa, musamman bayan da shugaban Napoli Aurelio De Laurentiis ya wallafa hoton Osimhen lokacin da ya ke sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa da kungiyare zuwa kakar wasa ta 2026.

Napoli dai ta sanya farashin yuro miliyan 100 a matsayin kudaden da kungiyoyi za su biya gabanin basu damar sayen Osimhen gabanin karewar kwantiraginsa.

Sai dai duk da wannan yarjejeniya, har yanzu kungiyoyi na rububin sayen Osimhen mai shekaru 25 lura da yadda bayanai ke cewa abu ne mai wuya ya ci gaba da zama a kungiyar bayan kakar wasa ta 2024.

Yanzu haka dai ana alakanta Osimhen da kungiyoyi irinsu Manchester United da PSG da kuma Real Madrid baya ga Liverpool baya ga ita Chelsea da kuma Arsenal wadanda suka mika tayin yuro miliyan 90 don sayenshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.