Isa ga babban shafi
AFCON

Masar ta kori mai horas da tawagar kasar bayan fiddasu daga AFCON

Hukumar Kula da Kwallon kafa ta kasar Masar ta sanar da korar mai horas da tawagar kasar Rui Victoria daga aiki, bayan da aka fiddata daga gasar lashe kofin Afrika AFCON.

Rui Victoria, tsohon mai horas da tawagar kasar Masar da hukumar kula da kwallon kafar kasar ta kora daga aiki.
Rui Victoria, tsohon mai horas da tawagar kasar Masar da hukumar kula da kwallon kafar kasar ta kora daga aiki. © RFI HAUSA/AHMED ABBA
Talla

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce ta sallami Vitoria tare da dukkanin masu taimaka masa baki daya, inda ta ce tana yi wa dan asalin kasar Portugal din fatan alkhairi.

Haka nan hukumar ta bai wa tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta al-Ahly Mohamed Youssef rikon kwaryar tawagar, da Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo ta fidda daga gasar AFCON a makon daya gabata.

Al'ummar Masar sun ji rashin dadin fiddasu da aka yi daga gasar, ganin yadda taje Ivory Coast din ne da fatan lashe gasar a karo na farko tun shekarar 2010, shekara daya gabanin Mohamed Salah ya fara doka wa tawagar kasarsa wasa.

Tun a makon da ya gabata Hukumar Kula da Kwallon kafa ta Masar, ta bai wa ‘yan kasar hakuri saboda gaza cimma burinsu.

Vitoria da ya jagoranci tawagar tsawon shekaru biyu, na daga cikin masu horaswan da suka rasa aikinsu a gasar AFCON ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.