Isa ga babban shafi

Bellingham ya taimaka wa Real Madrid ta koma saman teburin Laligar spain

Jude Bellingham ya ci gaba da aikinsa na saka kwallaye a raga a wasan da Real Madrid ta lallasa Villarreal da ci 4 da 1, lamarin da ya mayar da ita saman teburin gasar La ligar Spain.

Jude Bellingham, médio do Real Madrid.
Jude Bellingham, médio do Real Madrid. © LUSA - HUGO DELGADO
Talla

Dan wasan tsakiyar na tawagar kwallon kafar Ingila ya saka wa wata kwallon da Luka Modric ya kawo kai, inda ya ci kwallonsa ta 13 a gasar ta Laliga a wannan kaka, a cikin minti na 25 da fara wasa.

Rodrygo ya kara kwallo ta biyu, sakamakon sauya hukuncin alkalin wasa, wanda ya ce an yi satar fage da na’urar VAR ta yi amma sai Jose Luis Morales ya farke wa Villarreal daya bayan hutu.

Sai dai Madrid ta ci gaba da taka wa Villarreal din birki, inda Brahim Diaz da Luka Modric suka ci kwallo daya kowanne, lamarin da ya bai wa Madrid maki uku, ya kuma sa ta koma saman teburin La liga.

A karshen makon da ya gabata ne Real Madrid ta buga canjaras 1 da 1 da Real Betis, abin da ya sa Girona ta maye gurbinta a matsayi na 1 bayan doke Barcelona 4 da 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.