Isa ga babban shafi

Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afrika

Dan wasan Najeriya Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon Afrika na wannan shekarar ta 2023, abin da ya karfafa matsayinsa a jerin manyan 'yan wasa na duniyar tamola.

Victor Osimhen
Victor Osimhen AFP - ALBERTO PIZZOLI
Talla

Osimhen wanda ke taka leda a Napoli ya doke Achraf Hakimi na Morocco da Mohamed Salah na Masar wajen lashe kyautar ta gwarzon Afrika.

An gudanar da bikin karrama gwarzon dan wasan na Afrika ne a birnin Marakesh na Morocco, kuma a karon farko kenan tun shekarar 1999 da wani dan wasa daga Najeriya ke lashe kyautar tun bayan Kanu Nwankwo.

A bangaren mata kuwa, Asisat Oshiola ta Najeriya kuma mai taka leda a Barcelona ce ta zama gwarzuwar 'yar wasan Afrika a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.