Isa ga babban shafi

Pogba zai fuskanci dakatarwar shekaru 4 kan ta'ammali da sinadaran kara kuzari

Tauraron Faransa da ya lashe kofin duniya a shekarar 2018, zai fuskanci dakatarwar shekaru 4 bayan gwaji ya tabbatar da yadda ya yi ta’ammali da kwayoyin kara kuzari.

Dan wasan na Juventus da ya lashewa Faransa kofin Duniya a 2018 ya na da mako guda don daukaka kara kan hukuncin.
Dan wasan na Juventus da ya lashewa Faransa kofin Duniya a 2018 ya na da mako guda don daukaka kara kan hukuncin. AP - Antonio Calanni
Talla

A jiya Juma’a ne gwajin da aka yi wa Pogba mai shekaru 30 ya tabbatar da samun sinadarin testosterone metabolites a cikin jininsa, lamarin da ke tabbatar da gwajin farko na hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta Italiya.

Tun a ranar 11 ga watan Satumban da ya gabata ne Pogba ke fuskantar dakatarwa bayan hukumar ta Italiya ta bankado ta’ammalinsa da kwayoyin kara kuzarin.

Karkashin dokokin kasa da kasa dai, bayan tabbatar da wannan gwaji, kenan Pogba wanda ya dokawa Faransa wasanni sau 91 zai fuskanci dakatarwa daga dukkanin harkokin wasanni na tsawon shekaru 4 ko da ya ke hukuncin zai iya raguwa idan ya bayar da hujjojin cewa bai yi ta’ammali da sinadaran na sanya kuzari ba.

Idan har bincike ya tabbatar da cewa dan wasan bai yi ta’ammali da kwayoyin kara kuzarin a lokacin wata gasa ba, ko kuma basu taimaka wajen kara masa karsashi a kowanne wasa ba, kai tsaye hukuncin zai iya raguwa zuwa watanni.

Wasu majiyoyi dai sun shaidawa jaridar "La Pioche's" cewa Pogba ya yi amfani da wasu sinadarai da likita ya bashi a Amurka lokacin jinyarsa ne wanda sanadiyyarsu aka samu sinadaran na testosterone metabolytes a cikin jininsa.

Yanzu haka dai dan wasan na Juventus na da kwanaki 7 don kalubalantar hukuncin wanda zai bada damar sake wani dogon bincike da zai shafe tsawon makwanni gabanin kammalawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.