Isa ga babban shafi

Masu Liverpool sun sayar da hannun jarin kungiyar ga Dynasty Equity

Kamfanin FSG da ke da mallakin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ya amince da sayar da wani bangare na hannayen jarin kungiyar da darajarsu ta kai fam miliyan 82 da fam miliyan 164 ga katafaren kamfanin zuba jari a bangaren wasanni na kasa da kasa da ake kira Dynasty Equity.

Manaja Jurgen Klopp da wasu 'yan wasa a sansanin atisayen Liverpool na Melwood.
Manaja Jurgen Klopp da wasu 'yan wasa a sansanin atisayen Liverpool na Melwood. AFP/Archives
Talla

Tun farko FSG da kansa ya yi shelar neman masu sayen wani bangare na hannayen jarin kungiyar a kokarin warware basukan bankin da suka yi ma ta katutu, duk da cewa mamallakan na Liverpool na son ci gaba da rike mafi rinjayen hannayen jarin don samun karfin fada aji a kungiyar.

Shugaban kamfanin na FSG Mike Gordon ya ce kamar ko yaushe kamfani na da karfin fada aji a Liverpool duk da yadda ya sayar da wani bangare na hannayen jarin.

Liverpool dai ta yi asarar fam miliyan 100 na kudaden shiga a lokacin annobar Covid-19 yayinda kuma club din ya kashe fam miliyan 50 wajen ginin sabon sansanin atisayensa na Kirkby da aka bude a 2020 sai kuma wasu fam miliyan 12 na daban da kungiyar ta sanya wajen sayen tsohon sansanin atisayenta na Melwood da ta bai wa tawagar mata.

Baya ga wannan, kungiyar ta kashe kudin da yawansa ya kai fam miliyan 145 wajen sayen ‘yan wasa irinsu Dominik Szoboszlai da Alexis Mac Allister da kuma Wataru Endo baya ga Ryan Gravenberch a kasuwar musayar 'yan wasan da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.