Isa ga babban shafi

Newcastle ta doke Manchester City da kwallo 1 mai ban haushi a gasar Carabao

Alexandre Isak ya zura kwallo 1 tilo da ta bai wa Newcastle United nasara a haduwarta da Manchester City cikin daren jiya Laraba, kwallon da ke matsayin ta farko da dan wasan ya zurawa kungiyar ta shi cikin wannan kaka.

Kocin Newcastle United Eddie Howe
Kocin Newcastle United Eddie Howe Action Images via Reuters - Lee Smith
Talla

Newcastle wadda ta yi rashin nasara a hannun Manchester United yayin wasan karshe na gasar ta cin kofin kalubale ko kuma Carabao a kakar da ta gabata, ta yi sauye-sauye har guda 10 a zubin ‘yan wasan ta na jiya idan an kwatanta da zubin tawagar da ta yi nasara kan Sheffield United da kwallaye 8 da nema.

Newcastle ta tsare gida matuka a haduwarta ta jiya musamman a zagayen farko lokacin da City ta rike wuta, amma kuma har aka tafi hutun rabin lokaci babu wanda ya iya zura kwallo.

A minti na 53 ne, Isak da taimakon Joelinton ya zura kwallon daya tilo duk kuwa da tarin sauye-sauye har guda 7 da Pep Guardiola ya yi a tawagar tasa wadda bisa al’ada aka saba ganin yadda ta ke mamaye wasa.

Mai horar da kungiyar ta Newcastle Eddie Howe ya ce ya na fatan tawagar ta yi nasara fiye da wadda ta yi a kakar wasan da ta gabata dukkanin wasannin da ta ke fafatawa a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.