Isa ga babban shafi

Al-Hilal na Saudiya ta yi wa Mbappe tayin Yuro miliyan 200 duk shekara

Kungiyar Al-Hilal ta Saudiya ta yi tayin Yuro miliyan 200 duk shekara ga shaharerren dan wasan PSG na kasar Faransa Kylian Mbappe a kwangilar da zata bashi damar Komawa Real Madrid a shekara mai zuwa.

Dan wasan PSG na Faransa Kylian Mbappé.
Dan wasan PSG na Faransa Kylian Mbappé. © YVES HERMAN/REUTERS
Talla

Mbappe, mai shekara 24, a halin yanzu yana taka-tsan-tsan waken tsawaita kwantiragin sa dake shirin kawo karshe da PSG, kuma kungiyar ta Ligue 1 ba ta sa shi cikin ‘yan wasan da suka yi balaguro zuwa Japan da Koriya ta Kudu domin tunkarar wasannin sharan fage na kaka mai zuwa ba.

Kwantiragin dan wasan zai kawo karshe ne na club dake gasar Ligue 1 na Faransa a lokacin bazara na shekarar 2024, kuma kawo yanzu yaki amincewa da tsawaita kwantaragin, inda ake alakanta shi da komawa Real Madrid.

Hakan ya sa masu Club din na PSG suka dage don ganin lallai sun siyar da shi idan har ba zai amincewa da sabon kwantaragi ba, inda suka ce sun gwammace su karbi kasa da fam miliyan 155 da suka biya Monaco wajen dauko shi a shekarar 2017, domin kada ya wuce kyauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.