Isa ga babban shafi

West Ham ta kawo karshen jiran lashe kofi na tsawon shekaru 43

West Ham United ta lashe kofin gasar 'Europa Conference League' bayan doke Fiorentina da 2-1 yayin karawar da suka yi a daren ranar Laraba.

'Yan wasan kungiyar West Ham United yayin murnar lashe kofin gasar Europa Conference League, bayan doke Fiorentina da kwallaye 2-1, a filin wasa na Eden Arena, da ke birnin Prague, Jamhuriyar Czech.
'Yan wasan kungiyar West Ham United yayin murnar lashe kofin gasar Europa Conference League, bayan doke Fiorentina da kwallaye 2-1, a filin wasa na Eden Arena, da ke birnin Prague, Jamhuriyar Czech. REUTERS - BERNADETT SZABO
Talla

Nasarar ta bai wa kungiyar ta West Ham damar kawo karshen zaman jiran lashe kofin wata babbar gasa da ta shafe shekaru 43 tana yi.

Wasan na ranar Laraba dai yayi zafi matuka, lamarin da ya kusan kai wa ga shiga zangon karin lokaci na mintuna 30 kowace kungiya na da kwallo guda, amma sai dan wasan West Ham J. Bowen ya jefa kwallo ta biyu a ragar Fiorentina da taimakon Lucas Paqueta.

Yayin tsokaci kan nasarar da suka samu, kocin West Ham David Moyes, wanda ya ruga da gudu cikin murna bayan tashi daga wasan karshen, ya ce ba zai iya misalta irin farin cikin da yake ciki ba.

Kafin West Ham, Moyes ya horas da kungiyoyi da dama da suka hada da, Preston North End, Everton, Manchester United, Real Sociedad da kuma Sunderland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.