Isa ga babban shafi

Mai yiwuwa Ronaldo ba zai buga wa Al-Nassr wasan farko a ranar Alhamis ba

Mai yiwuwa Cristiano Ronaldo ba zai fara buga wa Al-Nassr wasa a yau Alhamis ba, kamar yadda kungiyar ta tsara.

Cristiano Ronaldo yayin taron menama labarai, bayan kulla yarjejeniya da kungiyar Al Nassr ta Saudiya.
Cristiano Ronaldo yayin taron menama labarai, bayan kulla yarjejeniya da kungiyar Al Nassr ta Saudiya. AP - Amr Nabil
Talla

Cikas din dai ya biyo bayan hukuncin dakatar da Ronaldo  daga buga wasnni biyu da hukumar FA ta yi a kakar wasan da ta gabata, saboda fasa wayar wani magoyin bayan Everton da yayi  lokacin da yake daukar hotonsa.

Da farko ‘yan sanda sun gargadi Ronaldo bayan aukuwar lamarin a watan Afrilun shekarar 2022, yayin da kuma aka ci tarar sa fan 50,000.

Karkashin dokokin hukumar FIFA, duk hukuncin haramcin buga wasanni da hukumar kwallon kafar wata kasa ta yanke yana nan daram yana aiki, ko da kuwa dan wasan da aka ladabtar ya sauya shekarsa zuwa wata nahiya ta daban.

Har zuwa lokacin da Ronaldo ya rabu da Manchester United, bai tsallake buga wasanni biyun da hukumar FA ta haramta masa ba.

Hakan na nufin idan har wannan hukunci zai yi aiki, Crsitiano zai sa ya rasa buga wasan da Al-Nassr za ta fafata da Al-Shabab a ranar 14 ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.