Isa ga babban shafi

Manchester United ta fara laluben dan wasan gaba don maye gurbin Ronaldo

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya tabbatar da cewa kungiyar na neman sayan dan wasan gaba a watan Janairu domin maye gurbin Cristiano Ronaldo da ya bar kungiyar a watan jiya.

Cristiano Ronaldo ya samu matsala tsakaninsa da mai horarwa Erik ten Hag wanda ya kai ga raba garinsa da kungiyar tun gabanin karewar kwantiraginsa.
Cristiano Ronaldo ya samu matsala tsakaninsa da mai horarwa Erik ten Hag wanda ya kai ga raba garinsa da kungiyar tun gabanin karewar kwantiraginsa. REUTERS - PHIL NOBLE
Talla

Tafiyar Ronaldo ta sanya a halin yanzu Ten Hag ba shi da zabi illa sanya Anthony Martial da Marcus Rashford a matsayin 'yan wasan sa na gaba.

Sai dai yayin wata ganawa da manema labarai kocin na United ya ce bai zama lallai su sami nasarar kullla yarjejeniya da dan wasan da su ke fata ba a nan kusa.

Duk da cewa suna tare da Ronaldo a farkon kakar wasan da mu ke, Manchester United ta yi fama da karancin cin kwallaye, abinda ya sa suka zama mafiya karancin zura kwallaye a tsakanin manyan kungiyoyin gasar Premier guda takwas, sai dai Ten Hag na da kwarin gwiwar Marcus Rashford, zai iya cike gurbin da Cristiano Ronaldo ya kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.