Isa ga babban shafi

Brazil na shirin bai wa Zinadine Zidane aikin horar da tawagar kasar

Rahotanni daga wasu majiyoyi a Brazil sun ce akwai yiwuwar hukumar kwallon kafar kasar ta bai wa Zinaden Zidane aikin horas da tawagar kwallon kafar kasar, bayan gaza kai wa wasan karshe da suka yi a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Qatar.

Da yiwuwar Zinedine Zidane ya zama sabon kocin Brazil.
Da yiwuwar Zinedine Zidane ya zama sabon kocin Brazil. AP - Martin Meissner
Talla

Croatia ce dai ta fitar da Brazil a zagayen kwata Final, rashin nasarar da ta sanya kocin tawagar kasar Tite ya ajiye aiki.

Jaridar L’equipe ta Faransa ta ruwaito cewar Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil CBF, ta na nazari kan zabin daukar sabon kocin ‘yan wasan kasar daga waje, kuma tsohon Zidane ke kan gaba a jerin sunayensu.

Tuni dai aka alakanta masu horaswa irin su Carlo Ancelloti na Real Madrid da Jose Mourinho na AS Roma da tawagar kwallon ta Brazil.

Yayin horas da Real Madrid Zidane ya samu nasara kafa tarihin lashe kofin gasar zakarun Turai sau uku a jere a shekarun 2016 da 2017 da kuma 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.