Isa ga babban shafi

Ingila ta rushe mafarkin Senegal a gasar cin kofin duniya

Ingila za ta fafata da Faransa a wasan dab da na kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar, bayan ta doke Senegal da ci 3-0.

'Yan wasan Ingila kenan da suke taya Bukayo Saka murnar zura kwallo a ragar Senegal
'Yan wasan Ingila kenan da suke taya Bukayo Saka murnar zura kwallo a ragar Senegal REUTERS - KAI PFAFFENBACH
Talla

Tawagar Gareth Southgate ta tsallake rijiya da baya a filin wasa na Al Bayt kafin Jordan Henderson da Harry Kane suka far wa Senegal kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bukayo Saka ne ya zura kwallo ta uku a ragar Senegal, amma kwazon da Bellingham ya taimakawa Ingila kasancewa ja gaba a wasan.

Bellingham ne ya taimakawa Henderson kuma dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund ya zura kwallon farko, inda daga bisani kyaftin din Ingila Harry Kane ya ci kwallonsa ta farko a gasar cin kofin duniya.

A yanzu Kane ya zura kwallo 11 a manyan gasa, inda ya wuce Gary Lineker a matsayin wanda ya fi kowa zura kwallo ga kasar.

shekarar 1966, bayan da ya riga ya bayyana kwarewar sa a fagen kwallon kafa ta duniya inda ya ci kwallonsa ta farko da Ingila ta doke Iran da ci 6-2 a rukuni.

Zakarun Afirka Senegal da farko ba su nuna fargaba ba yayin da suka matsawa tawagar Ingila, kafin daga bisani kuma lamura suka sauya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.