Isa ga babban shafi

Kolo Toure ya zama sabon kocin Wigan Athletics

Kungiyar kwallon kafar Wigan Athletics dake Ingila ta nada Kolo Toure, tsohon dan wasan kungiyar Arsenal da Manchester City da kuma Liverpool, a matsayin sabon manajan ta domin maye gurbin Leam Richardson wanda ya kawo karshen aikinsa. 

Tsohon dan wasan Manchester Ciy, Kolo Toure
Tsohon dan wasan Manchester Ciy, Kolo Toure mercatopsg.fr
Talla

Toure mai shekaru 41 ya rattaba hannu akan kwangilar shekaru 3 da rabi, abinda ya kawo karshen aikin taimakawa Brendan Rodgers, manajan kungiyar Leicester City tun daga shekarar 2019. 

Tsohon ‘dan wasan Cote d’Ivoire, Toure ya dade yana aiki tare da Rodgers wanda ya horas da shi a kungiyoyin Liverpool da Celtic, kafin ya dauke shi a matsayin mai taimaka masa. 

Kolo Toure wanda ke cikin tawagar ‘yan wasan Arsenal da suka kafa tarihi kammala kakar wasanni ba tare da barar da wasa koda guda ba, yace darussan da ya samu lokacin da yake aiki tare da Rodgers zasu taimaka masa wajen sauke nauyin aikin da aka dora masa a Wigan. 

Toure ya bayyana matukar farin cikinsa da nadin da aka masa, lura da cewar Wigan ba karamar kungiya bace dake da dimbin magoya bayan da yake sa ran su taimaka masa wajen samun nasara. 

Yanzu haka Wigan na matsayi na 22 a teburin Championship saboda lashe wasanni 6 kacal daga cikin 21 da ta buga a wannan kakar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.