Isa ga babban shafi

Da yiwuwar rauni ya hana Neymar doka sauran wasannin Brazil a Qatar

Kyaftin din Brazil Neymar ya ji rauni a idon sawunsa a wasan da tawagar kasarsa ta buga da Serbia a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar, kuma bayan wasan ne likitan tawagar ya ce za ayi masa a gwaji nan da sa’o’i 48.

Neymar ya samu raunin ne bayan taho-mugamar da ya yi da dan wasan baya na Serbia.
Neymar ya samu raunin ne bayan taho-mugamar da ya yi da dan wasan baya na Serbia. REUTERS - AMANDA PEROBELLI
Talla

Likitan, doctor Rodrigo Lasmar ya ce dan kasar Brazil din ya ji raunin ne bayan da ya yi karo da abokin hamayarsa na Serbia.

A cikin minti na 79 aka sauya Neymar a wasan da Brazil suka ci Serbia din 2 da 0.

An hango Neymar ya na dingisawa bayan wasan, a yayin hotunan da aka dauka suka nuna yadda idon sawunsa na dama ya kumbura.

Kocin Brazil, Tite ya ce dan wasan gaban na Paris Saint Germain ya ci gaba da wasan ko bayan ya ji raunin ne saboda matukar bukatarsa da tawagar ke yi a lokacin.

Ya kuma kawar da duk wata fargabar cewa dan wasan mai shekaru 30 zai iya zaman jinya har tsawon lokacin da za a kammala gasar cin kofin duniya.

Saura kwallaye biyu ne kawai Neymar ya ke nema ya cimma kwallaye 77 da Pele ya ci wa Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.