Isa ga babban shafi

Ghana ta sha alwashin fusata Ronaldo ta hanyar lallasa Portugal a wasansu

Tawagar kwallon kafar Ghana Black stars ta ce ta shiryawa haduwa da Cristiano Ronaldo na Portugal a karawarsu ta yau talata, domin kuwa baza ta nuna masa sassauci ba, dai dai lokacin da tawagogin biyu kowacce ke shirin doka wasan farko karkashin gasar ta cin kofin Duniya da ke ci gaba da gudana a Qatar.

Karawar Portugal da Ghana a shekarar 2014, wasan da Ghana ta yi rashin nasara da kwallo 1 da 2 bayan kwallon Ronaldo ta karshe a Brazil.
Karawar Portugal da Ghana a shekarar 2014, wasan da Ghana ta yi rashin nasara da kwallo 1 da 2 bayan kwallon Ronaldo ta karshe a Brazil. REUTERS/Jorge Silva
Talla

Tawagar ta Ghana da ke kunshi da tarin matasan ‘yan wasa galibi da ke shirin doka wasansu na farko karkashin gasar cin kofin Duniya, ta ce ko kadan ba za ta yi sassauci a karawar ta yau ba, kawai za ta shiga ne don samun nasara.

Kyaftin din tawagar ta Ghana Andrew Ayew ya yi ikirarin cewa ko shakka babu za su fusata Portugal a haduwar ta yau kwatankwacin yadda Saudi Arabia ta fusata Argentina.

A cewar Ayew, Black Stars suna dauke da matasan ‘yan kwallo majiya karfi da za su baiwa Portugal mamaki.

Yayin wasan na yau dai Portugal na shirin amfani da Cristiano Ronaldo wanda ya raba gari da Manchester United cikin makon nan.

Sau daya dai Ghana ta taba haduwa da Portugal a tarihi yayin wasannin gasar cin kofin Duniyar da ya gudana a Brazil a shekarar 2014 inda Portugal ta yi nasara da kwallaye 2 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.