Isa ga babban shafi

Saudiya ta bada hutu a daukacin kasar saboda doke Argentina

Babban Hadimin Masallatan nan biyu masu alfarma na Makka da Madina, wato Sarki Salman na Saudiya ya bada umarnin hutu a gobe Laraba ga daukacin ma'aikatan kasar baki daya sakamakon nasarar da kasar ta samu ta doke Argetina da kwallaye 2-1 a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

'Yan Saudiya na murnar samun nasarar doke Argentina
'Yan Saudiya na murnar samun nasarar doke Argentina © Saudigazette
Talla

Kazalika hutun ya shafi daukacin daliban makarantu da kamfanoni masu zaman kansu duk dai don nuna murnar doke Argentina wadda ke cikin bakin-cikin kashin da ta sha.

Yarima Mai Jiran Gadon Saudiya, Mohammed bin Salman, shi ne ya bada shawarar bada hutun-game garin.

Tawagar kwallon kafa ta Saudiya da ake kira Green Falcons ta kunyata gwarzon dan wasan duniya, wato Lionel Messi a wasan wanda ya gaza ceto kasarsa daga hannun Saudiya.

Argentina ce ta fara zuwa kwallo ta hannun Messi a bugun fanariti a minti  na 10 da saka wasan, amma Saudiya ta farke ta hannun Saleh Al-Shehri a minti na 48, kafin  Salem Al Dawsari ya kara ta biyu a minti na 53.

Tuni masharhanta suka bayyana wannan nasarar ta Saudiya a matsayin wani gagarumin al’amari da ya girgiza duniyar tamola.

Saudiya dai, ita ce kasa ta 51 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya, yayin da Argentina ke matsayin na 3, sannan kuma ta taba lashe kofin duniyar har sau biyu.

Argentina na cikin manyan kasashen duniya da ake sa ran za su taka gagarumar rawa a yayin gasar ta cin kfin duniya a Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.