Isa ga babban shafi

Sadio Mane baya cikin tawagar Senegal da zasu fafata a Qatar

Tauraron dan kwallon kafar Senegal, Sadio Mane, ba zai samu damar zuwa gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Qatar, bayan da da farko a sanya sunansa cikin ‘yan wasan duk da cewa yana fama da rauni.

Dan wasan Senegal Sadio mané
Dan wasan Senegal Sadio mané AFP - KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Sanarwar da hukumar kwallon kafar Senegal ta fitar ta nuna cewa an cire sunan dan wasan ne saboda bai samu murmurewa daga raunin guiwa da ya samu cikin sauri ba.

Kungiyarsa ta Bayern Munich dai tace Mane mai shekaru 30, wanda aka zaba a matsayin na biyu a kyautar Ballon d'Or a watan da ya gabata bayan Karim Benzema, an yi masa aikin tiyata "cikin nasara" kuma zai fara hutun murmurewa a Munich nan da 'yan kwanaki masu zuwa".

Rashin Mane a wannan gasa dai babbar komawa baya ne ga tawagar Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.