Isa ga babban shafi
Wasanni

Infantino ya bukaci tsagaita wuta a yakin Ukraine har kammala gasar Qatar

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino, ya yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su tsagaita bude wuta na wata guda saboda gasar cin kofin duniya da zai gudana a Qatar.

Shugaban Fifa, Gianni Infantino tare da sarkin Qatar , Tamim ben Hamad Al-Thani.
Shugaban Fifa, Gianni Infantino tare da sarkin Qatar , Tamim ben Hamad Al-Thani. AP - Hassan Ammar
Talla

Infantino ya shaidawa shugabannin a taron kolin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 a Indonesia cewa gasar cin kofin duniya na samar da wani “tsari na musamman” kan zaman lafiya da hadin kai domin mutane kimanin biliyan biyar ne za su kalli gasar ta talabijin.

Ya ba da shawarar wasu hanyoyin jin kai "ko duk wani abu da zai kai ga bude hanyar tattaunawa" a matsayin matakin farko na zaman lafiya.

A ranar Lahadi ne za a fara gasar cin kofin duniya a kasar Qatar, a daidai lokacin da ake ta sukar masu shirya gasar da take hakkin dan Adam a kasar musamman ma’aikatan da sukayi aikin gina filayen wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.