Isa ga babban shafi

An tafka kuskure da aka baiwa Qatar damar karbar gasar cin kofin Duniya- Blatter

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Sepp Blatter ya ce an tafka babban kuskure wajen bai wa Qatar damar karbar bakuncin gasar lashe kofin duniya ta bana.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA Sepp Blatter.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA Sepp Blatter. AFP
Talla

Blatter, mai shekaru 86 a duniya, shike shugabantar hukumar FIFA lokacin da aka baiwa Qatar karbar bakuncin gasar a shekarar 2010.

Kasar dai na shan suka game da matsayar ta na hana masu auren jinsi gudanar da mu’amular su a lokacin gasar, da kuma zargin cin zarafin ma’aikata ‘yan cirani a kasar.

Blatter ya ce Qatar karamar kasa ce, gasar lashe kofin duniya ya mata girma ta amshi bakoncin sa.

Blatter ya ce ko a lokacin zaben, Amurka ya zaba, sai dai ya dora alhakin bai wa Qatar damar daukar nauyin gasar a wuyan tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini.

Wannan ne karo na farko da wata kasa daga yankin gabas ta tsakiya ke samun damar karbar bakoncin gasar a cikin shekaru 92 duk da kasancewar kasashen nahiyar a matsayin 'yan gaba-gaba da ke zuba makudan kudi a abin da ya shafi kwallon kafa.

Haka zalika wannan ne karon farko da za a gudanar da wannan gasa a yanayin hunturu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.