Isa ga babban shafi

Kotu ta samu dan wasan Jamus Jerome Boateng da laifin dukan budurwarsa

Kotu a Jamus ta tabbatar da laifin cin zarafi kan fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Jerome Boateng, wanda ake tuhuma da laifin dukan tsohuwar budurwarsa a shekarar 2018.

Mai tsaron baya na tawagar kwallon kafar Jamus Jerome Boateng.
Mai tsaron baya na tawagar kwallon kafar Jamus Jerome Boateng. © Reuters
Talla

A shekarar da ta gabata kotu ta samu Boateng da laifin cin zarafin tsohuwar abokiyar zamansa, mahaifiyar ‘ya’yansa tagwaye mata, a lokacin hutun Caribbean shekaru hudu da suka wuce, makwanni bayan kammala gasar cin kofin duniya a Rasha.

Sai dai Kotun da ke gundumar Munich ta rage yawan tarar da  a baya aka bukaci Jerome Boateng ya biya daga euro miliyan 1.8 zuwa euro miliyan 1.2.

Dan wasan dai ya sha musanta zarge-zargen da ake yi masa tare da daukaka karar neman wanke shi daga tuhumar.

Yayin zaman farko na shari’ar da aka musu, tsohuwar Sahibar Boateng ta shaidawa kotun cewa dan wasan ya krba mata naushin da saboda karfinta, wanda hakan ya sa ta rasa numfashi na dan wani lokaci yayin wata zazzafar muhawara da ta kaure tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.