Isa ga babban shafi

Spain: Masu gabatar da kara sun janye tuhumar da ake yiwa Neymar

Masu gabatar da kara a Spain sun yi watsi da zargin cin hanci da rashawa da zamba da ake yi wa dan wasan Brazil, Neymar.

Dan wasan tun farko ya ce bashi da masaniya kan yadd aka kulla yarjejeniyar komawarsa Barcelona
Dan wasan tun farko ya ce bashi da masaniya kan yadd aka kulla yarjejeniyar komawarsa Barcelona REUTERS - ALBERT GEA
Talla

Ana tuhumar dan wasan gaban Paris St-Germain da kuma wasu a shari’ar da aka yi masa kan cinikinsa daga kungiyar Santos zuwa Barcelona a shekara ta 2013.

Da farko dai masu gabatar da kara sun nemi daurin shekaru biyu a gidan yari da kuma tarar Yuro miliyan 10 ga matashin mai shekaru 30.

Amma sun sanar da janye tuhumar da ake yi wa “dukkan wadanda ake tuhuma bisa rashin kwararan hujjoji kan zarge-zargen da suke fuskanta.

Sauran wadanda ake tuhuma a karar sun hada da iyayen Neymar, kungiyoyin biyu, da tsoffin shugabannin Barcelona Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell, da kuma tsohon shugaban kungiyar Santos Odilio Rodrigues.

Neymar, wanda ya musanta zargin, ya ce ba zai iya tuna lokacin da aka kulla wata yarjejeniyar da ta sabawa oka da shi ba. A shekara ta 2011 ne aka cimma matsaya kan tafiyarsa daga Santos zuwa Barcelona, wanda aka kammala shekaru biyu bayan haka.

Barcelona ta ce a wancan lokaci an yi cinikin Neymar kan kudin Yuro miliyan 57.1, inda aka biya iyalansa Yuro miliyan 40 daga ciki sai kuma tsohuwar kungiyarsa da ta samu kashi 40% na ragowar Euro miliyan 17.1 da aka biya wa kulob din Santos na Brazil.

Dan wasan na Brazil ya yi rashin nasara a daukaka kara a babbar kotun Spain a shekarar 2017, wanda ya kai ga gabatar da kara na Spain gurfanar da shi.

Masu gabatar da kara dai sun nemi daurin shekaru biyar ga Rosell, da kuma tarar kudi Yuro miliyan 8.4 ga Barcelona, da kuma hukuncin daurin shekara biyu kan Neymar da tarar Yuro miliyan 10.

Sai dai Baker McKenzie, lauyoyin da ke kare dangin Neymar, sun yi ikirarin cewa kotunan kasar Spain ba su da hurumin gurfanar da dangin Neymar da kamfaninsu N&N” saboda ‘yan kasar Brazil ne suka aikata wannan aika-aika a wajen kasar Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.