Isa ga babban shafi

Argentina ta yi bikin karbar rigar da Maradona ya saka a gasar cin kofin duniya

Al’ummar Argentina na bikin murnar komawar rigar da Diego Maradona ya saka a wasan karshe na gasar cin kofin duniya

Rigar da Maradona ya sanya a wasan da suka samu nasara kan Ingila, yayin gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986.
Rigar da Maradona ya sanya a wasan da suka samu nasara kan Ingila, yayin gasar cin kofin duniya ta shekarar 1986. © AFP Photo/Sotheby's
Talla

Shekaru 36 kenan bayan da Argentina ta doke Jamus a gasar cin kofin duniya da aka yi a 1986, kuma rigar da dan wasan ya saka a wancan lokacin yanzu haka an mikawa hukumar kwallon kafar kasar ita, domin adana ta cikin kayayyakin tarihi.

Tsohon dan wasan tsakiya na kasar Jamus, Lothar Matthäus wanda suka yi musayar rigar da Maradona bayan an tafi hutun rabin lokaci, ya sadaukar da it aga al’ummar Argentina.

Wata rigar Maradona, wacce ya saka a lokacin da ya zura kwallo a ragar Ingila a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya a shekarar 1986, an sayar da ita a kan dala miliyan 7.1 a farkon wannan shekarar. Tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Steve Hodge ne ya yi gwanjon rigar, haka zalika a kwanan nan ne aka yi gwanjon wata kwallo da dan wasan ya yi amfani da ita wajen zura kwallo a ragar Ingila a gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.