Isa ga babban shafi

Champions League: Messi ya fice daga tawagar da za ta fafata da Benfica

Lionel Messi baya cikin tawagar ‘yan wasan Paris St-Germain da za su kara da Benfica a gasar cin kofin zakarun Turai gobe Talata saboda raunin da ya ji.

Dan wasan Paris St-Germain kenan Lionel Messi.
Dan wasan Paris St-Germain kenan Lionel Messi. REUTERS - RONEN ZVULUN
Talla

Messi, mai shekaru 35, ya zura kwallo a fafatawar da suka yi a Portugal a makon da ya gabata, kafin daga bisani aka cire shi.

Har ila yau, dan wasan na Argentina, bai buga karawar da suka tashi kunnen doki da Reims a gasar Ligue 1 ranar Asabar ba inda PSG ta gaza samun nasara a gasar a karon farko a bana.

PSG ce ke kan gaba a rukunin H da maki bakwai, inda Benfica ke biye mata, sai Juventus ta uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.