Juventus ta ce ta yi asarar kudi Yuro miliyan 254 a kakar bana
Kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke kasar Italiya, ta ce ta yi asarar zunzurutun kudi har Yuro miliyan 254 a wannan shekarar, sakamakon koma baya da ta samu wajen samun kudaden shiga da kuma hauhawar farashin kayayyaki.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne a karon farko da kungiyar ta karkare kaka ba tare da samun nasarar lashe ko da kofi guda ba.
A wata sanarwa da ta fitar, Juventus tace za ta karkare wannan kaka ta 2022-23 cikin yanayi na rashin kudi, duba da cewa har yanzu tana jin radadin annobar Covid -19.
Wannan ce shekara ta 5 a jere da wannan kungiya da ke wasa a gasar Serie A ta Italiya ke sanar da faduwa, kuma na wannan karo ya zarta ta kakar 2020-21.
Wannan matsalar kuma ta zo daidai ne da lokacin da kungiyar ke rashin katabus a gasar Italiya ta wannan shekarar, inda take matsayi na 8 a teburin Serie A.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu