Isa ga babban shafi

Amnesty ta nemi FIFA ta biya diyyar ma'aikatan da aka ci zarafinsu a Qatar

Sakamakon wani aikin tattara kuri’ar jin ra’ayi da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta gudanar, ya gano cewa galibin masoya gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya na goyon bayan FIFA ta biya bakin haure ma’aikata diyya saboda cin zarafin da ake yi musu a lokacin shirye-shiryen gasar da za a yi a Qatar a karshen shekarar da muke ciki ta 2022.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, Gianni Infantino. AFP - CYRIL NDEGEYA
Talla

Kafin fitar da wannan sakamako a jiya Alhamis, Qatar ta sha fuskantar suka kan zarginta da ake yi mata da rashin mutunta hakkokin ma’aikata bakin-haure da ake amfani da su wajen shirye-shiryen fara gasar cin kofin duniya da za ta karbi bakunci.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'ar da aka yi wa take da ''YouGov'' ta tattara ra’ayoyin mutane fiye da dubu 17,000 daga kasashe 15, akasarinsu a Turai, sai kuma da Amurka da Mexico da Argentina da Morocco da kuma Kenya.

Yayin da ta ke mayar da martani kan rahoton na Amnesty International, hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta za ta yi nazari kan binciken, amma ta yi gargadin cewa "mutanen da suka bayyana ra’ayoyinsu ba su da cikakkiyar masaniya game da matakan da jami’an FIFA da na Qatar suka aiwatar a 'yan shekarun nan don kare hakkokin ma'aikatan dake da ruwa da tsaki a shirye shiryen gasar cin kofin duniya ta FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.