Isa ga babban shafi

Buhari ya karrama 'yar wasan tseren Najeriya, Tobi Amusan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika kyautar Naira miliyan 200 na karramawar kasa ga tawagar ‘yan wasan Najeriya da suka fafata a gasar wasannin Commonwealth da gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka gudanar a bana.

Tobi Amusan lokacin da take karbar lambar yabo daga shugaban Najeriya muhammadu Buhari
Tobi Amusan lokacin da take karbar lambar yabo daga shugaban Najeriya muhammadu Buhari © punch
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Abuja yayin da yake jawabi a wajen liyafar karrama ‘yan wasan da shugaban fadar shugaban ta shirya.

Buhari ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ba da kyauta mai kyau, ba ma dai ga 'yan kungiyar ta Najeriya da suka kunna kaimi ga nasara a cikin al'ummar kasar ta hanyar baje kolin su na basira a wasannin kasa da kasa.

Ministan matasa da ci gaban wasanni Sunday Dare, ya bayyana shekarar 2022 a matsayin shekarar da ta yi fice a tarihin wasannin Najeriya, wadda ba za a manta da ita ba.

Dare ya ce a fagen guje-guje da tsalle-tsalle, Amusan a cikin watanni hudu ta lashe lambar zinare ta farko ga Najeriya a gasar ta duniya kuwa da aka yi a Eugene, da ke yankin Oregon, a Amurka ‘yar wasan ta kafa tarihi a gasar da Turawa suka mamaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.