Isa ga babban shafi

Chelsea za ta fara tattaunawa da Graham Potter don bashi aikin horarwa

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shirya tattaunawa da mai horar da ‘yan wasan Brighton, Graham Potter a wani yunkuri na maye gurbin Thomas Tuchel da shi, kwana guda bayan korar mai horarwa da ya shafe watanni 20 yana jan ragamar Stamford Bridge.

Mannajan kungiyar kwallon kafa ta Brighton Graham Potter da Chelsea ke shirin dauka aikin horar da 'yan wasanta.
Mannajan kungiyar kwallon kafa ta Brighton Graham Potter da Chelsea ke shirin dauka aikin horar da 'yan wasanta. AFP
Talla

A jiya Laraba ne Chelsea ta sallami Thomas Tuchel, wanda ya lashe mata kofuna 3 a cikin watanni 20, korar da ke zuwa bayan rashin nasara a wasan farko da ya jagoranta karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Tuni dai Brighton ta bai wa Potter mai shekaru 47 wanda tsohon kocin Swansea Ostersunds FK ne izinin tattaunawa da Chelsea.

An sallami Tuchel ne bayan da ‘yan wasan Chelsea da ma sabon ma maallakin kungiyar suka yi masa yankan kauna.

Potter, wanda ake ganin shi zai kasance mai horar da ‘yan wasan Ingila a nan gaba ya jagoranci Brighton zuwa matsayi na 4 a teburin Firimiya  a wannan kaka da aka fara.

A watan Mayun shekarar 2019 ne aka nada shi kocin Brighton, kuma ya kai kungiyar zuwa ga  kammalawa a matsayi na 15, 16 da kuma 9 a shekaru 3 da ya yi tare da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.