Isa ga babban shafi

Cristiano Ronaldo zai kasance a tawagar United da za ta fafata da Rayo Vallecano

Cristiano Ronaldo ya nuna cewa zai taka rawa a wasan sada zumunci da Manchester United za ta yi da Rayo Vallecano a Old Trafford ranar Lahadi.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. AP - Dave Thompson
Talla

Dan wasan na Portugal din yana son United ta bar shi ya sauya sheka haka zalika bai kasance cikin tawagar da suka fafata a wasan wasan kungiyar daa Thailand da Australia ba saboda wasu dalilai na kashin kansa.

Ronaldo, mai shekaru 37, kuma ba ya cikin tawagar United da za ta buga wasan sada zumunta da Atletico Madrid a Oslo ranar Asabar.

Amma ya  bayyana a shafin Instagram cewa zai kara da Rayo Vallecano ta La Ligar Spain.

Ronaldo ya gana da kocin United Erik ten Hag a ranar Talata kuma an fahimci cewa ya sake nanata sha’awarsa na barin Old Trafford.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.