Isa ga babban shafi

Roma ta sayi dan wasan gaba na Ghana Felix Afena-Gyan

Kungiyar kwallon kafa ta Roma mai doka gasar Serie A a Italiya ta sanar da kulla yarejejeniya da dan wasan gaba na Ghana Felix Afena-Gyan yau Alhamis daga karamar tawagar kungiyar.

Felix Afena-Gyan ya zurawa Roma kwallaye 2 a wasanni 22 da ya doka.
Felix Afena-Gyan ya zurawa Roma kwallaye 2 a wasanni 22 da ya doka. © AFP - OZAN KOSE
Talla

Dan wasan mai shekaru 19 daya zurawa kwallaye 2 a wasanni 22 cikin kakar da ta gabata, sanarwar ta Roma ta ce yau alhamis ne ya amince da rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru 4, wanda ke zuwa bayan gwajin amfani da shi a babbar tawaga cikin watan Oktoba.

A jawabinsa bayan kammala sanya hannu akan kwantiragin, Afena-Gyan ya ce tun bayan da ya isa Roma, fatansa shi ne taka leda a babbar tawagar.

Acewar dan wasan wanda ya dokawa Ghana wasan farko cikin watan Maris din da ya gabata tare da taimakwa kasar sa samun gurbi a gasar cin kofin Duniya, yayin nasarar zura kwallonsa ta farko ne ga kasarsa a wasansu da Madagascar.

A shekarar 2021 ne Afena-Gyan ya je Roma inda ya fara taka leda karkashin tawagar ‘yan kasa da shekaru 18 amma kuma sannu sannu ya koma koma fara take leda karkashin Jose Mourinho a tawagar manya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.