Isa ga babban shafi

Pogba na shirin komawa Juventus kyauta daga United

Paul Pogba na shirin komawa Juventus a kyauta bayan kwantiraginsa a Manchester United ya kare, inda rahotanni suka ce dan wasan tsakiyar Faransa mai shekaru 29, zai yi gwajin lafiyarsa a karshen mako kafin ya kammala komen.

Dan wasan Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba. AFP/File
Talla

Pogba ya koma United ne daga Italiya a shekarar 2016 kan kudi mafi tsada a duniya a lokacin wato fam miliyan 89.

Gaza cimma matsaya

United da Pogba sun kasa cimma matsaya kan sabon kwantaragi kuma a farkon watan Yuni kungiyar ta tabbatar da cewa zai bar ta a matsayin dan wasa mai cin gashin kansa a wannan bazarar.

Ana sa ran Pogba zai fara atisaye da Juventus a mako mai zuwa kafin tafiya Amurka, inda za su kara da Barcelona da Real Madrid a ranakun 27 da 30 ga watan Yuli.

Juventus

A kakar wasa ta biyu a jere, Juventus ta kare a mataki na hudu a gasar Seria A da maki 16 tsakaninta da AC Milan mai rike da kofin gasar.

Sun kasance zakarun Italiya a kakar wasanni tara da suka gabata, inda Pogba ya taka muhimmiyar rawa a nasarar da suka samu daga kakar 2012-13 da kuma 2015-16.

Ya zura kwallaye 34 a wasanni 178 a baya tare da Jubentus sannan ya koma United kyauta a shekarar 2012.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.