Isa ga babban shafi

Ronaldo ya roki United ta sallame shi zai yi gaba

Cristiano Ronaldo ya bukaci kungiyar da yake dokawa wasa yanzu haka Manchester United da ya yi wa Allah ta barshi ya yi gaba, muddun har ta samu tayin da ya dace da shi.

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo.
Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo. AP - Bernadett Szabo
Talla

Dan wasan gaban na Portugal, mai shekaru 37, ya koma Old Trafford daga Juventus a bazarar da ta wuce.

Duk da cewa Ronaldo, shine dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a kakar wasan da ta wuce - kuma na uku a gasar Premier - ana kallon kakar wasannin da ta shude a matsayin babbar koma baya a gareshi.

United ta kare a matsayi na shida a teburin Premier don haka ta rasa tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai.

Hakan na nufin Ronaldo, wanda ke da sauran kwantiragin shekara daya da United, zai fuskanci doka wasannin gasar Europa a karon farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.