Isa ga babban shafi

Manchester United ta yi watsi da tayin Barcelona kan Maguire

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi watsi da tayin Barcelona ta Spain kan dan wasanta na baya Harry Maguire a wata yarjejeniyar musaya a kokarin da kungiyar ke yi na kawo Frankie de Jong Old Trafford.

Dan wasan Manchester United Harry Maguire.
Dan wasan Manchester United Harry Maguire. AFP
Talla

Duk da tayi mai gwabi da Barca ta yi ga Maguire wanda United ta saya kan yuro miliyan 80 matsayin dan wasan baya mafi tsada, kungiyar ta ki amincewa maimakon haka ta yi na’am da farashin yuro miliyan 69 ga de Jong.

Sabon Manajan United, Erik Ten Hag ya bayyana cewa Maguire na cikin ‘yan wasan da ya ke son shafe lokaci ya na aiki tare da su a Old Trafford, haka zalika shi kansa dan wasan baya son raba gari da kungiyar.

Akwai dai yiwuwar kungiyoyin biyu su iya cimma jituwa kafin kulle kasuwar musayar ‘yan wasa dai dai lokacin da Ten Hag ke fatan amfani da de Jong a wasannin ran gadin shiga sabuwar kaka da kungiyar ta Ingila za ta yi tattaki zuwa kasashen Thailand da Australia a karshen makon gobe.

Baya ga de Jong Manchester United na harin Christian Eriksen dan Denmark da ke taka leda da Brentford.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.