Isa ga babban shafi

Kasashen Turai na shirin fara doka gasar Natione League karo na 3

Gobe Laraba 1 ga watan Yuni ake shirin fara gasar kwallon kafar UEFA Nations League na shekarar 2022-2023 tsakanin kasashen Turai.

Kofin gasar Nations da za a fara gobe laraba tsakanin kasashen Turai.
Kofin gasar Nations da za a fara gobe laraba tsakanin kasashen Turai. REUTERS/Pierre Albouy
Talla

Gasar ta wannan karo ta cike gibin da aka samu ne na gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a irin wannan lokaci, amma a wannan karo aka dage zuwa watan Nuwamba saboda tsananin zafin da ake fama da shi a kasar Qatar.

Ita dai wannan gasa da ake bugawa kowacce shekara, ta na bai wa kasashen Turai damar karawa a tsakaninsu, kuma wannan shi ne karo na 3 da za a gudanar.

Kasar Portugal ta lashe gasar farko a shekarar 2019, yayinda Faransa ta lashe kofin bara bayan doke Spain a wasan karshe.

Kasar Poland za ta fara wasan farko da Wales gobe alhamis, yayin da Arewacin Ireland za ta kara da Girka a ranar alhamis.

A ranar Asabar Hungary za ta kara da Ingila, yayinda Armenia za ta kara da Jamhuriyar Ireland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.