Isa ga babban shafi

Gwamnatin Burtaniya ta ba da izinin sayar da kungiyar Chelsea

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da amincewa da shirin hamshakin attajirin Amurka Todd Boehly na sayen kungiyar Chelsea daga hannun takwaransa na Rasha Roman Abramovich da aka laftawa takunkumi.

Todd Boehly, hamshakin attajirin Amurka da ke shirin sayen Chelsea.
Todd Boehly, hamshakin attajirin Amurka da ke shirin sayen Chelsea. © AP - Mark J. Terrill
Talla

Tun a ranar 7 ga watan Mayun da ya gabata ne dai, attajiri Boehly yayi tayin sayen Chelsea kan fam biliyan 4 da miliyan 25, don sayan kulob din daga Abramovich.

A farkon watan Maris ne dai Abramovich ya saka Chelsea a kasuwa, kafin gwamnatin Burtaniya ta lafta masa takunkumi sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, sai dai an yi ta jan kafa wajen kammala cinikayyar saida kungiyar ta Chelsea, sakamakon yadda gwamnatin Birtaniya ba ta son attajirin na Rasha ya amfana da riba daga cinikin.

Abramovich, wanda ita ma Kungiyar Tarayyar Turai EU ta kakabawa takunkumi, gwamnatin Birtaniya ta bayyana shi a matsayin makusancin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Sayar da Chelsea mai rike da kofin gasar cin zakarun Turai ta kakar wasan shekarar 2021, ya kawo karshen shekaru 19 na nasarorin da ba ta taba samu ba a karkashin Roman Abramovich mai shekaru 55, wanda ya jagoranci kungiyar wajen lashe kofunan Firimiya biyar da na gasar zakarun Turai biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.