Isa ga babban shafi
Rasha - wasanni

Rasha na neman damar shirya gasar cin kofin Turai a 2028

Rasha ta shiga cikin sahun jerin kasashen da ke gogayyar samun izinin karbar kakuncin kofin nahiyar Turai a shekarar 2028 da kuma 2032, duk da dakatarwar da ita da aka yi mata biyo bayan mamayar da tayi a Ukraine.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tare da wasu jagororin hukumar kwallon kafar duniya FIFA.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tare da wasu jagororin hukumar kwallon kafar duniya FIFA. © REUTERS
Talla

A ranar Laraban nan ce dai hukumar shirya wasannin nahiryar Turai ta bayyana sunayen kasashen da suka nuna sha’awar su na karbar bakuncin gasar inda kasashen Rasha da Turkiya da Ingila da kuma Ireland ne dai za su yi gogayya wajen neman karbar bakuncin gasar na shekarar 2028.

A watan Satunba ne ake saran hukumar UEFA za ta sanar da kasar da zata amshi bakuncin gasar.

Rasha ita ce dai ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2018 sannan aka tsaida gudanar da wasan karshe na lashe kofin zakarun nahiyar Turai a wannan shekarar a can, sai dai daga baya aka sauya saboda mamayar da ta yi a Ukraine.

Turkiya na saran karbar bakuncin gasar bayan da ta yi rashin nasara a wajen Jamus da zata amsa bakuncin gasar na shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.