Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Abu ne mai wuya Ronaldo ya ci gaba da zama a Manchester United

Masana na ganin abu ne mai wuya dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya amince da ci gaba da taka leda da kungiyar matukar ta gaza samun gurbi a gasar cin kofin zakarun Turai na kaka mai zuwa.

Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo.
Dan wasan gaba na Portugal Cristiano Ronaldo. © AFP - OLI SCARFF
Talla

Rashin nasara United a hannun Manchester City ranar lahadi da kwallaye 4 da 1 da ke matsayin rashin nasara karo na biyu karkashin kocin rikon kwarya Ralf Rangnick ya diga ayar tambaya kan matsalar jagorancin da kungiyar ke fama da shi da ke matsayin barazana ‘yan wasanta.

Ba kadai Ronaldo ba, hatta Marcus Rashaford da ke da sauran shekara guda a kwantiaginsa da kuma zabin iya tsawaita yarjejeniyar ya bayyanawa manema labarai cewa idan abubuwa basu sauya a kungiyar kai tsaye zai shafi wasanninsa a matakin kasa wanda kuma dole ya nemi mafita akai.

A baya-bayan nan ne Rashford ya sanar da aniyar ci gaba da taka leda da Manchester United amma kuma ko a wasan na ranar lahadi mai horarwa Rangnick ya ajje shi a benci duk da yadda wasan ya gudana ba tare da Ronaldo na Portugal ba haka zalka Edinson cavani.

Tun bayan karbar ragamar da Ralf Rangnick ya yi wasanni 8 cikin 18 kadai United ta yi nasara a karkashinsa.

Ronaldo mai shekaru 37 da ya sha alwashin ganin kungiyar tasa ta kammala firimiyar bana a sahun ‘yan ukun saman teburi don samun gurbi a gasar zakarun Turai ta badi wasu bayanai na alakanta shi da kungiyar kwallon kafa ta PSG matakin da zai bashi damar hadewa da tsohon abokin dabinsa Lionel Messi.

Yanzu haka dai United na da sauran wasanni 10 karkashin gasar ciki har da tattakinta zuwa gidajen Liverpool da Arsenal gabanin karbar bakoncin Tottenham da Chelsea kuma a tsakankanin wadannan wasannin ne take bukatar maki mai tarin yawa don shiga sahun ‘yan hudu.

Rashin iya samun gurbi a gasar zakarun Turai dai zai haddasawa Manchester United manyan matsaloli ciki har da iya gaza lallamar ‘yan wasa su ci gaba da zama da su ciki har da Paul Pogba da tun tuni ya ke shirin raba gari da kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.