Isa ga babban shafi
Wasanni - Rasha - Ukraine

UEFA za ta yi taron gaggawa kan yakin Rasha da Ukraine

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai UEFA za ta gudanar da taron gaggawa a ranar Juma'a 25 ga watan Fabarairu, domin tantance halin da ake ciki dangane da mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine, da kuma shirin karbar bakuncin wasan karshe na gasar zakarun Turai da za a yi a Saint Petersburg cikin watan Mayu.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, Aleksander Ceferin.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, Aleksander Ceferin. © Juilliart/UEFA/Handout via REUTERS
Talla

A ranar 28 ga watan Mayu ne ake sa ran za a buga wasan karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai a filin wasa na Gazprom Arena da ke birnin Saint Petersburg, wanda tuni aka gudanar da wasanni da dama cikin filin a gasar cin kofin nahiyar Turai da aka yi a bara, da kuma gasar cin kofin duniya ta 2018 da ta gudana a kasar Rasha.

A shekarun baya dai sau biyu hukumar UEFA ta sauya filayen da ya kamata a buga wasannin karshe na gasar Zakarun Turai saboda annobar Korona daga Istanbul zuwa Lisbon a shekarar 2020, sannan kuma daga birnin na Turkiya zuwa Porto a 2021

Lokaci na karshe da kasar Rasha ta karbi bakuncin wasan karshe na gasar cin kofin Zakarun Turai shi ne a shekarar 2008, lokacin da Manchester United ta doke Chelsea a bugun fanariti a birnin Moscow.

A ranar Talatar da ta gabata, Fira Ministan Birtaniya Boris Johnson ya ce Rasha ba ta da wata damar gudanarwa ko karbar bakuncin wasannin kwallon kafa a Turai idan ta mamaye Ukraine.

A halin yanzu akwai kungiyoyi hudu na gasar Firimiyar Ingila da ke cigaba da fafatawa a gasar zakarun Turai ta bana, wadanda suka hada da Chelsea da Manchester City, Manchester United da kuma Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.